Iran-Birtaniya

Birtaniya ta zargi Iran da yunkurin kwace mata jirgin ruwa a tekun Fasha

Alaka ta kara tsami tsakanin Birtaniya da Iran tun bayan da Tehran ta zargi London da sace mata jirgin ruwa a makon jiya
Alaka ta kara tsami tsakanin Birtaniya da Iran tun bayan da Tehran ta zargi London da sace mata jirgin ruwa a makon jiya Reuters

Gwamnatin Birtaniya ta fitar da sanarwar cewa, wasu jiragen ruwa Iran 3 sun yi kokarin kwace mata tankar mai a tekun Fasha yau Alhamis, mako guda bayan Birtaniyar ta kwace wata tankar man Iran da ta yi zargin ta na kokarin shigar da mai Syria.

Talla

Ma’aikatar tsaron Birtaniya ta bayyana cewa, sai da aka yi gwagwarmaya tsakanin jami’an sojin ruwan Birtaniya da ke tsaron tankar man da matukan kwale-kwalen 3 har ta kai ga barazanar harbi kafin bayar da dama ga tankar ta wuce a tekun fasha.

Wata majiyar Amurka da ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a gab da arewacin mashigar ruwan Hormuz.

Yunkurin kwace tankar wadda Iran ta musanta hannu a ciki ya kara dada tsamin alaka tsakanin Birtaniyar da Iran tun bayan zargin kwace jirgin daukar mai da Iran din ke yiwa Birtaniya, bayan da ta zargi kasar da yunkurin karya takunkuman da ke kanta wajen shigar da mai Syria.

Cikin kalaman shugaban rundunar sojin juyin juya halin Iran Ali Fadayi ya bayyana cewa basu da masaniya kan yunkurin kwace jirgin, sai dai ya nanata cewa tabbas Amurka da Birtaniya za su dandana kudarsu kan ci gaba da rike jirgin Iran.

Ko a jiya Laraba dai, Birtaniya ta nanata cewa Iran da kanta ta sace jirginta.

Tuni dai Iran ta sake fitar da wani sabon gargadi ga kassahen na Birtaniya da Amurka inda ta ke cewa tabbas za su yi nadamar abin da su ka aikata game dajirginta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.