May-Amurka

May ta caccaki Trump kan muzanta 'yan Majalisun Amurka mata

Firaministar Birtaniya mai barin gado Theresa May da shugaban Amurka Donald Trump
Firaministar Birtaniya mai barin gado Theresa May da shugaban Amurka Donald Trump Reuters

Firaministan Birtaniya mai barin gado Theresa May, ta yi TUR da kalaman batancin da shugaban Amurka Donald Trump ya furta kan wasu ‘yan majalisun kasarsa mata 'yan jam’iyyar Democrats, wadanda ya bukaci da su koma kasashen da suka fito marasa manufa da kuma fama da cin hanci.

Talla

Tuni dai 'yan takarar shugabancin Amurka na jam’iyyar Democrats da sauran yan majalisu suka yi A wadai da kalaman na Trump da ya wallafa a ranar lahadi, inda suka bayyana kalaman a matsayin nuna wariyar jinsi, saboda rashin kasancewarsu Amurkawa.

Shugaban na Amurka ya taba haddasa irin wannan cece-kuce a shekarar bara, lokacin da ya kamanta kasashen Afrika da shadda, tare da bayyana kwarar bakin-haure cikin Amurka a matsayin mamaya.

Yan majalisun mata da Trump ke nufi da kalaman dai sun hada da Alexandria Ocasio-Cortez daga New York, Ilhan Omar da ke wakiltar Minnesota, Rashida Tlaib daga Michigan da kuma Ayanna Pressley mai wakiltar Massachussets.

Trump ya zargi yan majalisun da shisshigi wajen nunawa Amurkawa yadda za a tafiyar da gwamnatinsu mafi karfi da tsari a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.