Turai-Iran

Shugabannin Turai sun bukaci tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran

Wani sashin cibiyar Bushehr ta sarrafa makamashin nukiliya na Uranium da ke Teheran babban birnin kasar Iran.
Wani sashin cibiyar Bushehr ta sarrafa makamashin nukiliya na Uranium da ke Teheran babban birnin kasar Iran. AFP/HAMED MALEKPOUR

Manyan shugabannin kasashen Turai uku sun bukaci tattaunawar sulhu, don kawo karshen tsamin dangantakar Amurka da Iran da ta haddasa musayar zafafan kalamai tsakaninsu, kan yarjejeniyar nukiliyar 2015.

Talla

Shugabannin Faransa, Jamus da kuma Birtaniya ne suka gabatar da tayin tattaunawar a jiya lahadi, bayan wata ganawar da suka yi a birnin Paris inda suka halarci bikin zagayowar ranar juyin juya halin kasar ta Bastille.

Kasashen sun yi gargadin cewa yarjejeniyar nukiliyarta Iran na fuskantar barzanar rushewa muddin ba’a gaggauta ceto ta ba, matakin da suka ce Iran na dagagarumar gudunmawa wajen aiwatar da shi.

A baya bayan nan dai ya tabbata cewa Iran ta karya daya daga cikin ka’idojin yarjejeniyar nukiliyarta 2015 ta hanyar kara yawan makamashin Uranium da take tacewa.

Matakin na Iran kuma ya biyo bayan tsaikon aiwatar da alkawarin saukaka mata tasirin takunkuman da Amurka ta kakaba mata, da manyan kasashen da ke cikin yarjejeniyar suka dauka, lamarin da ya kara tsamin dangantakar da ke tsakanin Iran din da Amurkan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.