Isa ga babban shafi
Lafiya

Yara miliyan 20 basu samu rigakafin cutuka ba a 2018 - MDD

Yara dubu 350 ne suka kamu da cutar kyanda a shekarar 2018.
Yara dubu 350 ne suka kamu da cutar kyanda a shekarar 2018. Reuters/Lindsey Wasson
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla yara miliyan 20 a fadin duniya ne ba a iya yiwa rigakafin kamuwa da cututtuka ba a shekarar 2018 da ta gabata.

Talla

Rahoton ya bulla ne yayin da karuwar masu kamuwa da cutar kyanda a baya bayan nan ke haifar da fargaba.

Rahoton na shekara shekara da Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma Hukumar UNICEF suka gabatar, ya ce yara kusan miliyan 19 da rabi ne basu samu rigakafin ba, adadin da ya dara na shekarar 2017 inda aka samu sama da miliyan 18 da rabi.

Hukumar UNICEF ta kara da cewa akalla yara dubu 350 ne suka kamu da cutar kyanda a shekarar bara, ninkin wadanda suka kamu da cutar a shekarar 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.