Faransa da Rasha sun sha alwashin ceto Yarjejeniyar nukiliyar Iran
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Rasha Vladmir Putin sun cimma matsayar hada karfi don ceto yarjejeniyar nukiliyar da Iran ta cimma da manyan kasashen Duniya daga rushewa.Matakin ya biyo bayan yadda lamura ke dada zazzafa a yankin gabas ta tsakiya, musamman tsakanin Iran da Amurka.
Wallafawa ranar:
A jiya alhamis ne Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaran sa na Rasha Vladmir Poutine suka cimma daidaito don ceto yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen Duniya.
Shugabanin na Faransa da Rasha sun tattauna ta wayar talho tareda jaddada goyan bayan su na ganin an cimma matsalha cikin ruwan sanyi tsakanin Iran da Amurka.
Majiya daga fadar Kremlin daga kasar Rasha na nuni cewa Shugaban Faransa Emmanuel Macron ne ya kira takwaran sa na Rasha, matakin da Vladmir Poutine ya yaba da shi, yayinda Macron ya tsaya kai da fata cewa nauyi ya rataya wuyan kasashen Turai, tareda rakiyar manyan kasashe da suka hada da Rasha da China don tabbatar da yarjejeniyar nukiliya ta shekara ta 2015,tareda yi kira zuwa Iran na ganin ta mutunta alkawuran da ta dau a baya, da kuma zai taimaka don sake farfado da tattalin arzikin kasar ta Iran.
A farkon watan Yuli ne Iran ta sanar da janyewa daga yarjejeniyar, tareda daukar alkawarin inganta makamashin nukiliyar ta, Ministan harakokin wajen Jamus Helko Maas a jiya alhamis ya bayana mamakin sa ganin janyewar Amurka daga wannan yarjejeniyar, inda ya kuma yi kira zuwa Iran na ta yiwa Allah ta mutunta wannan yarjejeniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu