Cuba ta yafewa Fursunoni fiye da dubu 3 zaman gidan kaso

Shugaba Miguel Diaz-Canel na Cuba
Shugaba Miguel Diaz-Canel na Cuba ADALBERTO ROQUE / AFP

Gwamnatin Cuba ta sanar da saki wasu fursunoni kimanin dubu 2 da 604, a karkashin wani shirin yafiya, wanda shi ne irinsa na farko da ya dubunnan fursunoni suka ci gajiyarsa cikin shekaru 4.

Talla

Rahotanni sun bayyana cewa Fursunonin da suka ci gajiyar shirin yafiyar na Gwamnati Galibi, sun kammala wa’adin uku bisa hudun zamansu na wakafi kan laifukan da suka aikata.

Ka zalika shirin sakin fursunonin bai sahale sallamar wadanda aka tuhuma tareda yankewa hukunci kan manyan laifuka da suka kunshi ko dai Fyade ko kuma Kisan kai ba.

Wannan dai ne karon farko da shugaba Miguel Diaz-Canel ke yafiya ga tarin fursunoni tun bayan hawansa mulki a watan Aprilun 2018, haka zalika shi ne mafi girman yafiya da kasar ta taba yi tun bayan yafiyar fursunoni akalla dubu 3 da 522 da shugaba Raul Castro ya yi a shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.