Birtaniya ta roki Iran ta sakar mata jiragen mai

Guda cikin jiragen ruwan Birtaniya da Iran ta kwace
Guda cikin jiragen ruwan Birtaniya da Iran ta kwace JAN VERHOOG / AFP / MARINETRAFFIC.COM

Birtaniya ta roki Iran kan ta sakar mata jiragen man ta har guda 2 da ta sanar da kamewa a shekaran jiya Juma’a, a wani mataki da Birtaniyan ke cewa ta hakan ne kawai Iran za ta yayyafa ruwa a rikicin da yankin gabas ta tsakiya ke fuskanta.

Talla

Cikin wani sakon Bidiyo na ministan wajen Birtaniyar Jeremy Hunt, ya ce kwace tankar na diga ayar tambaya ga tsaron mashigar ruwan na Hormuz musamman domin masu dakon man fetur.

Sai dai Iran ta yi watsi da kiran kasashen Turai wajen ganin ta saki tankokin bisa cewa sun karya ka’idojin shige-da fice, dai dai lokacin da Amurka ke kokarin girke tarin dakarunta a yankin wadanda Saudiya wadda ke matsayin abokiyar dabin Tehran za ta karbe su.

A juma'ar da ta gabata ne, Jami'an tsaron juyin juya halin Iran suka sanar da kame jiragen biyu na Birtaniya a mashigin ruwan Hormouz.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.