Amurka

Amurka ta maido da hukuncin kisa kan masu laifi

Wani gidan yari a California da ke Amurka
Wani gidan yari a California da ke Amurka REUTERS/Stephen Lam/File Photo

Gwamnatin Amurka ta bayyana shirinta na maido da aiwatar da hukuncin kisa kan masu aikata miyagun laifuka bayan shekaru 16 da dakatar da hukuncin. Babban Lauyan Gwamnatin kasar, Bill Barr ya ce, tuni aka tsayar da ranar fara aiwatar da hukuncin kan wasu mutane biyar da aka same su da laifin kisan-kai.

Talla

A yayin cika umarnin shugaban Amurka Donald Trump na daukan tsattsauran mataki kan miyagun laifuka, Babban Lauyan Gwamnatin kasar, Bill Barr ya umarci Hukumar Kula da Gidan Yarin kasar da ta bullo da sabon tsarin yi wa masu laifin allurar guba don raba su da rayuwarsu.

Barr ya ce, Ma’aikatar Shari’ar Kasar na goyon bayan dokokin kasar, kuma tilas ne su aiwatar da dokokin domin yin adalci ga ‘yan uwa da iyalan wadanda aka zalunta a cewarsa.

A bara dai, an samu hukunce-hukuncen kisa har guda 25, inda hukumomin jihohi daban daban suka aiwatar da hukuncin.

Sai dai an dauki tsawon lokaci ana tafka muhuawara a game da hanyoyin aiwatar da kisan, yayinda tsohuwar gwamnatin Barack Obama ta ki bayyana matsayinta a game da hukuncin, abinda ya sa tun shekarar 2003, aka

samu tsaikon aiwatar da kisan kan furfusonin da aka garkame a gidajen yarin gwamnatin tarayya.

A halin yanzu dai, akwai mutane 62 a matakin gwamnatin tarayya da hukuncin kisan ya hau kansu da suka hada da mutumin nan da ya kashe mutane uku a harin bam din birnin Boston a shekarar 2013 a yayin gasar tseren fanfalaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI