Kotu ta bai wa Trump damar gina katanga da kudin Gwamnati

Donald Trump na Amurka a gaban nau'in katangar da ya ke fatan ginawa a kan iyakar kasar da Mexico
Donald Trump na Amurka a gaban nau'in katangar da ya ke fatan ginawa a kan iyakar kasar da Mexico REUTERS/Kevin Lamarque/File Photo

Kotun Kolin Amurka ta bai wa shugaban kasar Donald Trump damar amfani da dala biliyan 2 da rabi daga asusun ajiyar kasar wajen gina wani banagren na Katanga a kan iyakar kasar ta kudanci.

Talla

Kotun a zaman shari’ar da ta gudanar ta yi watsi da umarnin kotun birnin California da ta haramtawa shugaban amfani da kudin wajen ginin katangar.

Ginin katangar wadda za ta raba Amurka ta Mexico na daga cikin manyan alkawuran da Trump ya daukarwa Amurkawa kafin zabensa a matsayin shugaban kasa a shekarar 2016, kudirin da ke fuskantar kakkausar suka daga jam’iyyar adawa ta Democract.

Hukuncin kotun dai na nuni da cewa yanzu haka aikin ginin Katangar zai kankama gadan-gadan a biranen California da Arizona da kuma New Mexico.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.