Duniya

Taron cimma sabuwar matsaya a yarjejeniyar Nukiliyar Iran

Tutar kasar Iran a harabar zauren taron hukumar dake kula da yada makamai masu guba  a Vienna
Tutar kasar Iran a harabar zauren taron hukumar dake kula da yada makamai masu guba a Vienna REUTERS/Lisi Niesner

A yau lahadi kasashe dake da hannu a batun yarjejeniyar nukiliyar Iran za su gudanar da wani taron su Vienna  na kasar Austria da nufin ceto yarjejeniyar tun bayan da Amurka ta sanar da yi watsi da mataki biyo bayan zargin kasar Iran da rashin mutunta alkawuran da ta dau a baya.

Talla

A farkon watan Janairu ne Iran ta yi watsi da kiraye-kirayen da manyan kasashen duniya suka yi mata na yin biyayya ga yarjejeniyar da aka kulla da ita a shekarar ta 2015 na takaita adadin makamashin Uranium da take yi.

Ita dai kasar Iran ta kafe ne da matsayinta na ranar 8 ga watan 5 cewa, zata yi watsi da yarjejeniyar da aka kulla da ita saboda yadda shugaban Amurka Donald Trump ya kara kirba mata takunkumin karairaya ta, bayan da shi ma Trump ya janye daga yarjejeniyar tun a bara.

Shugaban Iran Hassan Rouhani yace matakin su ya biyo bayan rashin cika alkawari ne da aka nuna masu, gashi kuma an gaza yin komi dangane da takunkumin da Amurkan ta malkaya mata.

Adadin makamashin Nukiliyan da aka bari Iran ta mallaka dai zai bata damar samarda hasken wutan lantarki, wanda ba a taba kai adadin bukatar samar da nukiliya ba.

Kasar Iran dake fuskantar mantsin lamba ta fuskar tattalin arzikli ,kasashen Faransa, Birtaniya, Jamus, Rasha da China na sa ran a zaman nay au cimma wata matsaya da za ta taimaka don samar da sassauci daga kowane bangare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI