Isa ga babban shafi
Faransa-Iran

Macron ya gana da Rouhani kan rikicin Iran da Amurka

Donald Trump, Emmanuel Macron da Hassan Rouhani
Donald Trump, Emmanuel Macron da Hassan Rouhani .
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Bashir Ibrahim Idris
1 Minti

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tattauna da shugaban kasar Iran Hassan Rouhani a kokarin da yake yi na sasanta rikicin da ke tsakanin kasar da Amurka.

Talla

Fadar shugaban Faransa ta ce, shugabannin biyu sun tattauna ne ta wayar tarho a kokarin da kasar ke yi na daukar duk matakan da suka dace na ganin bangarorin sun bude kofar tattaunawa.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sha alwashin kokarin sasanta bangarorin biyu domin rage tankiyar da ake samu da kuma ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran da ke neman rugujewa sakamakon janyewar Amurka da kuma dorawa Iran sabbin takunkumin karayar tattalin arziki.

Fadar shugaban Faransa ta ce, shugaba Macron ya yi doguwar tattaunawa da shugaba Rouhani lokacin da yake hutunsa na shekara a Bregancon da ke gabar ruwan Meditereniya, inda ya sake jaddada muhimmancin rage tankiyar da ake samu.

Sau biyu jakadan da ke bai wa shugaba Macron shawara kan harkokin waje Emmanuel Bonne ke zuwa birnin Tehran domin ganawa da hukumomin kasar, yayinda ake saran shugaban Rasha Vladimir Putin shi ma zai ziyarci Macron a tsakiyar watan Agusta domin tattauna batun kafin taron G7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.