Amurka

An kashe dan Osama bin Laden

Hamza bin Laden
Hamza bin Laden FEDERATION FOR DEFENSE OF DEMOCRACIES / AFP

Hukumomin Amurka sun sanar da kashe dan Osama bin Laden, wato Hamza bin Laden da aka zaba domin jagorancin kungiyar Al Qaeda.

Talla

Kafofin yada labaran Amurka da suka hada da NBC da New York Times sun tabbatar da kashe Hamza kamar yadda jami’an gwamnatin Amurka suka sanar da su, inda suka ce ya mutu ne a yayin wani farmaki da kasar ke da hannu wajen kaddamar da shi.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ki cewa uffam game da kisan Hamza, yana mai cewa, ba ya son yin magana kan batun.

Rahotanni sun ce, an kashe dan Osaman ne kafin Amurka ta sanar da ware ladar Dala miliyan guda a watan Fabairu a matsayin tukuici kan duk wanda ya tsegunta mata maboyarsa.

Hamza ya sha fitar da sakwannin murya da bidiyo,i nda ya bukaci kaddamar da farmaki kan Amurka da wasu kasashen duniya a matsayin ramuwar gayya game da kishe mafaihinsa da Amurka ta yi a cikin watan Mayun shekarar 2011 a Pakistan.

Hamza mai shekaru 30, shi ne da na 15 daga cikin jumullar 'ya'ya 20 da Osama ya haifa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI