EU ta shure takunkuman Amurka kan ministan harkokin wajen Iran
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kungiyar Kasashen Turai ta yi fatali da takunkumin karya tattalin arzikin da Amurka ta sanyawa ministan harkokin wajen Iran, Javad Zarif, inda ta bayyana cewar za ta ci gaba da hulda da shi.
Carlos Martin De Gordejuela mai magana da yawun babbar jami’ar diflomasiyar kungiyar ta EU, Fedrico Mogherini, ya bayyana takaicin kungiyar kan matakin na Amurka, inda yace za su cigaba da aiki tare da Zarif.
Yayin da Amurka ke bayyana kakabawa ministan harkokin wajen na Iran takunkumin, mai baiwa shugaban kasar ta Amurka shawara kan harkokin tsaro John Bolton ya bayyana Zarif a matsayin haramcaccen mai Magana da yawun Iran.
Bolton ya kuma kara da cewa tabbas Iran kasa ce dake daukar nauyin ayyukan ta’addanci, ta hanyar daukar nauyin kungiyoyin ‘yan ta’adda da kuma basu makamai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu