Amurka

Amurka na makokin wadanda hare-haren bindiga ya kashe

Maharin birnin El Paso na jihar Texas Patrick Crusius lokacin da kyamarar tsaro ta dauke hotonsa yayin kai harin
Maharin birnin El Paso na jihar Texas Patrick Crusius lokacin da kyamarar tsaro ta dauke hotonsa yayin kai harin Courtesy of KTSM 9 / KTSM 9 news Channel / AFP

Shugaban Donald Trump na Amurka ya bukaci sauke tutocin kasar sakamakon kazamin hare haren yan bindiga da suka hallaka mutane 29 a kasar, dai dai lokacin da masu shigar da kara a birnin El Paso na jihar Texas ke neman kotu ta yankewa maharin birnin hukuncin kisa.

Talla

Amurkan dai ta fuskanci hare-haren ‘yan bindiga a jihohin Texas da California cikin kasa da sa’o’i 24 wanda ya hallaka jumullar mutane 29 wanda jami’an tsaro suka yi nasarar hallaka maharin California yayinda aka kame maharin Texas.

Masu shigar da kara a kasar ta Amurka dai na neman kotu ta tuhumi maharin na Texas wanda aka bayyana sunansa da Patrick Crusius mai shekaru 21 da laifin ta’addanci tare da yanke masa hukuncin kisa.

A cewar babban alkalin yankin El Paso a jihar Texas Jaime Esparza, yayin taron manema labaran da ya kira, maharin ya cancanci hukuncin kisa yana mai cewa suna fatan hakan ya tabbata a gaban kotu.

Jumullar wadanda hare-haren ya jikkata ya kai mutane 53 da ya kunshi 26 a Texas wasu 27 kuma a California, kuma dukkaninsu matasa ne jar fata suka kaddamar da su wanda shekarunsu bai haura 24 a duniya ba.

Harin dai ya faru ne tsakanin safiyar Asabar zuwa tsakaddare wanda ya faru a shagon sayayya na birnin El Paso a jihar Texas da kuma wata mashaya a California.

Bayan umarnin shugaban kasar Donald Trump mahukuntan Amurka sun sakko da tutar kasar kasa, da nufi jimami tare da makokin mutanen da suka rasa rayukansu a harin.

Harin bindiga dai ba sabon abu ba ne a kasar ta Amurka ko da dai ba safai aka fiya fuskantar hari biyu a lokaci guda da ya hallaka jama’a kamar haka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI