Venezuela

Amurka ta tilasta wa Maduro jingine tattaunawa

Shugaban Venezuela Nicholas Maduro
Shugaban Venezuela Nicholas Maduro Fuente: Reuters.

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya sanar da soke tattaunawar da wakilansa ke yi da bangaren 'yan adawa sakamakon sabbin takunkumin karayar tattalin arziki da Amurca ta kakaba wa kasarsa.

Talla

Sanarwar gwamnatin kasar ta ce, shugaba Maduro ya soke shirin tura tawagar wakilansa zuwa taron da aka shirya gudanarwa a yau Alhamis da gobe juma’a wanda kasar Norway ke jagoranci a Barbados.

Maduro ya danganta matakin da abinda ya kira tirsasawar da Amurka ke ci gaba da yi wa al’ummar kasar.

A bangare daya, dubban magoya bayan gwamnatin Venezuela ne suka gudanar da zanga-zangar Allah-wadai da Amurka a birnin Caracas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI