Saudiya

Miliyoyin Musulmai sun fara aikin hajji a Saudiya

Sama da Musulmin duniya miliyan 2 da rabi ne ke aikin hajjin bana a Saudiya
Sama da Musulmin duniya miliyan 2 da rabi ne ke aikin hajjin bana a Saudiya AHMAD AL-RUBAYE / AFP

Musulmi sama da milyan biyu da rabi daga sassa daban daban na duniya ne suka fara gudanar da aikin hajji, daya daga cikin shika-shikan addinin musulunci biyar a wannan juma’a.

Talla

Mahukunta a Saudiyya sun bullo da tsare-tsaren gudanar da aikin hajjin cikin sauki a bana, yayinda suka gargadi cewa za a dauki matakin ba sani ba sabo ga duk wanda ya yi yunkurin yin amfani da aikin hajji domin yada manufofinsa na siyasa, wannan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin kasashen yankin gabas ta tsakiya.

A zantawarsa da sashen hausa na RFI, Alhaji Oumarou Hama Diallo, shugaban kamfanin shirya aikin hajji na Badr kuma Sakataren Kawancen kamfanonin Cosapel da yanzu haka ke birnin Makka, ya ce tabbas a bana dauki matakai domin gudanar aikin hajjin a cikin tsari musamman don magance matsalar cinkoso.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren bayanin da Alhaji Diallo ya yi mana.

Alhaji Diallo kan aikin hajji a Saudiya

Mai magana da yawun rundunar sojin Saudiya, Bassam Attia ya ce, an kirge ilahirin jami’an tsaron kasar da suka hada da sojojin sama da na kasa don tabbatar da gudanar da aikin hajjin cikin kwanciyar hankali.

A gobe Asabar ne Mahajjatan za su hau arafa wanda shi ne rukuni mafi girma a aikin hajjin, yayinda sauran musulmin duniya za su dauki azumin nafila domin tarin falalar da ke cikinsa kamar yadda sunnar Manzan Allah ta koyar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.