Faransa

Ba ma bukatar izinin Amurka don sasanta rikicin nukiliya - Faransa

Ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian.
Ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian. REUTERS/Stephane Mahe/File Photo

Faransa ta ce bata bukatar neman izini daga wata kasa ko wani shugaba, don shiga kokarin sasanta rikicin Amurka da Iran da ke dada kamari.

Talla

Ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian ya bayyana haka, a lokacin da yake maidawa shugaban Amurka martani, bisa sukar Faransa da yayi kan yunkurin sasanta rikicin dake tsakaninsu da Iran, matakin da Trump ya bayyana a matsayin shisshigi.

Takaddama tsakkanin Faransa da Amurka na neman kunnu kai ne, a dai dai lokacin da manyan kasashen Turai ciki harda Faransar, Jamus da kuma Birtaniya, ke kokarin ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran daga rushewa, bayan da Amurka ta fice daga cikinta a shekarar bara, tare da laftawa Iran din takunkunman karya tattalin arziki.

A farkon watan Agusta, kungiyar kasashen Turai ta yi fatali da takunkumin karya tattalin arzikin da Amurka ta sanyawa ministan harkokin wajen Iran, Javad Zarif, inda ta bayyana cewar za ta ci gaba da hulda da shi.

Carlos Martin De Gordejuela mai magana da yawun babbar jami’ar diflomasiyar kungiyar ta EU, Fedrica Mogherini, ya bayyana takaicin kungiyar kan matakin na Amurka, inda yace za su ci gaba da aiki tare da Zarif.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.