EU- Korea ta Arewa

EU ta yi tur da gwajin makamin Koriya ta Arewa

Hoton sabon gwajin da Koriya ta Arewa ta yi.
Hoton sabon gwajin da Koriya ta Arewa ta yi. Jung Yeon-je / AFP

Kungiyar Tarayyar Turai ta yi tur da gwaje-gwajen makaman masu linzami da Koriya ta Arewa ta gudanar a baya-bayan nan, tana mai cewa, hakan ya yi hannun riga da kokarin kasashen duniya na samar da tsaro a yankin.

Talla

A karo na biyar kenan cikin makwanni biyu da kasar ke gudanar da gwajin makaman, yayinda shugaba Kim Jong Un ya bayyana gwajin a matsayin gargadi mai karfi game da atsayen sojin hadin guiwa tsakanin Koriya ta Kudu da Amurka.

Ma’aikatar tsaron Korea ta Kudu, ta ce makaman da Koriya ta Kudu ta yi gwajin, masu cin gajeren zango ne, wadanda suka yi tafiyar kilo mita 400 kafin fadawa yankin tekun da ke tsakaninsu da Japan.

A sanarwar da ta fitar, Kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci Koriya ta Arewa da ta kauce wa haifar da tashin hankali, sannan kuma ta mutunta alkawarinta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.