Al'ummar Musulmi na murnar Sallar layya a sassan duniya
Wallafawa ranar:
Yau lahadi 10 ga watan Zul Hijja shekara ta 1440 bayan hijirar Manzon Allah (SAW) daga Makka zuwa Birnin Madina, al’ummar Musulmi ke murnar Sallar Layya a sassan duniya.
Daya daga cikin abubuwa mafi muhimmanci a wanna rana shi ne yanka dabbobin layya ga wadanda suka samu dama, bayan halartar Sallar Idi.
A wannan rana da wadanda ke tafe, masu wadata ken sada zumuntar rabar da wani yanki na naman da suka yanka, domin dadawa wadanda basu samu damar yin layya ba.
A jiya asabar ne dai al’ummar Musulmi sama da miliyan 2 da ke halartar aikin Hajjin bana suka yi hawan Arfa, daya daga cikin ginshikan ibadar dake cikin jerin shika shikan Addinin Musulunci, yayinda a sassan duniya ragowar al’ummar Muslumin ke azumtar wannan rana.
Musulmi na amfani da damarmakin na aikin Hajji da murnar Sallar ta layya wajen gudanar da addu’o’in zaman lafiya a sassan duniya.
Yayin bukukuwan jama’a na samun damar sada zumunci da ‘yan uwa da abokan arziki, wadanda a wasu lokutan akan dauki lokaci mai tsawo ba tare da an gana ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu