Isa ga babban shafi
Isra'ila

Isra'ila na shan caccaka kan hana 'yan majalisar Amurka shigarta

'Yan majalisar wakilan Amurka Musulmi Ilhan Omar, da Rashida Tlaib, daga tsakiya, sai kuma shugaban Amurka Donald Trump da Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
'Yan majalisar wakilan Amurka Musulmi Ilhan Omar, da Rashida Tlaib, daga tsakiya, sai kuma shugaban Amurka Donald Trump da Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. REUTERS/File Photos
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Matakin Isra’ila na hana wasu mata Musulmi ‘yan majalisar dokokin Amurka shiga kasar, ya janyo mata mummunan suka daga aminanta.

Talla

Sama da ‘yan Majalisun Amurka 70 ne karkashin jam’iyyar Democrat suka fito karara suka soki matakin Isra’ilar na hana Ilhan Omar da Rashida Tlaib shiga cikinta.

Kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi da ba ta jituwa da ‘yan majalisun a lokuta da dama, a wannan karon ta ce bayyana matakin na Isra’ila a matsayin abinda bai dace ba.

Matan biyu sun yi fice wajen sukar gwamnatin Isra’ila, sai dai sun musanta zargin nuna kiyayya ga yahudawa.

Cikin watan Yuli shugaban Amurka Donald Trump ya sake jaddada matsayinsa kan ‘yan majalisun kasar mata guda 4 dake cigaba da sukar manufofinsa, inda yace idan basu gamsu da rayuwa a Amurka ba, su fice su koma kasar su.

Yayin jawabi a fadar shugaban kasa, Trump ya bayyana ‘yan majalisun da suka hada da Ilhan Omar, Alexandria Ocasio-Cortez da Ayyana Pressley da kuma Rashida Tlaib, a matsayin gwanayen korafi, wadanda basa son Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.