Damisoshi na barazanar karewa a dazukan Duniya

Damisa
Damisa Pixabay/CC

Wani rahoton kungiyar da ke rajin kare namun daji a duniya, ta bayyana yadda ake ci gaba da fuskantar kamfar damisa wadanda ke ci gaba da karewa a dazukan nahiyar Asia, sakamakon abin da ta kira safararsu da ake ba bisa ka’ida ba dama kisansu da wasu ke yi.

Talla

Rahoton kungiyar ya nuna yadda fiye da damisa dubu 2 da dari 3 suka yi batan dabo a dazukan nahiyar ta Asiya, ciki har da wadanda aka hallaka.

Rahoton ya nuna cewa akalla damisa 120 ake safara kowacce shekara daga nahiyar zuwa wasu sassa na duniya wanda ke nuna cewa ana safarar akalla damisoshi 2 a kowanne mako.

A cewar rahoton wanda ya dora alhakin bacewar damisoshin kan hukumomin kula da gandun dajin kasashen na Asiya, ya tun daga shekarar 2000 ne duniya ta fara fuskantar matsalar ta bacewar damisoshi.

Kanitha Krishnasamy, mawallafin rahoton, ya bayyana cewa yadda adadin damisohin da ke bacewar ke kara yawa babban abin damuwa ne ga makomar nau’in halittar wanda ke matsayin wani yunkurin shafesu a ban kasa.

Krishnasamy ya bayyana cewa cikin shekarun 1900 fiye da damisoshi dubu 100 ne ke yawo a ban kasa, amma rahoton 2010 ya nuna yadda ake da adadin damisoshin da basu gaza dubu 3 da 200 a ban kasa ba, sakamakon yadda ake farauta, hallaka su dama kisansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.