Turkiya-Rasha

Erdogan na shirin ziyartar Rasha game da hare-haren Syria

shugaba Recep Tayyip Erdogan.
shugaba Recep Tayyip Erdogan. AFP/Adem Altan

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan zai ziyarci birnin Moscow na Rasha a mako mai kamawa, ziyarar da ke zuwa bayan wasu hare-hare ta sama kan jerin gwanon motocin Sojin Turkiyan a Syria.

Talla

Ziyarar bazatan wadda Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanar da kansa a jiya juma’a ana ganin za ta mayar da hankali kan yadda dakarun Bashar al-Assad ke gab da kwace iko da yankin Idlib marikar ‘yan tawaye ta karshe a arewa maso yammacin Syrian.

Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov wanda ya sanar da ziyarar ta Erdogan a Rasha da zata gudana ranar 27 ga watan nan bai bayyana hakikanin makasudin ziyarar da kuma batutuwan da za a tattauna yayinta ba.

A bara dai kasashen Turkiya mai mara baya ga ‘yan tawaye da kuma Rasha babbar mai goyon bayan gwamnatin kasar, sun cimma yarjejeniyar ganin an kare fararen hula a yankin na Idlib.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.