Iran-Amurka

Ya yi wuri mu tattauna da Iran a yanzu- Trump

Donald Trump na Amurka a jawabinsa gaban manema labarai yayin taron G7 a Faransa.
Donald Trump na Amurka a jawabinsa gaban manema labarai yayin taron G7 a Faransa. REUTERS/Yves Herman

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yayi wuri ya gana da babban jami’in Diplomasiyyar Iran Mohammed Javad Zarif da ya yi yiwa taron G7 dirar mikiya a karshen makon nan, ya na mai cewa Amurka ba ta matsu a samar da sauyi kan halin da kasashen biyu ke ciki ba.

Talla

Yayin da ya ke tattaunawa da manema labarai yayin taron na G7 da ake karkarewa yau Litinin a birnin Biarritz na kudancin kasar Faransa, Trump ya ce basu damu da tattaunawa don samar da maslaha kan rikicinsu da Iran ba.

A cewar Trump ya na sane da cewa Javad Zaraf zai halarci taron, hasalima sai da Emmanuel Macron ya tuntube shi gabanin aike masa da sakon gayyata zuwa taron na G7, sai dai ya ce zuwan na sa bazai amfanar da komi game da tsamin alakar da ke tsakaninsu ba.

Shugaban na Amurka ya ce yana da cikakkiyar masaniya kan duk wani yunkuri daga takwaransa na Faransa Emmanuel Macron wajen ganin an samu daidaito tsakanin kasashen biyu musamman kan yarjejeniyar nukiliyar kasar.

A cewar Donald Trump ya aminta da kokarin Macron sai dai abin da Amurka tafi damuwa da shi a yanzu shi ne ganin ta wargaza duk wani yunkurin Iran na mallakar makamin nukiliya da nufin samar da cikakken tsaro a yankin gabas ta tsakiya.

Tsawon watanni kenan Emmanuel Macron na Faransa na kai ruwa rana wajen ganin an samu daidaito tsakanin Amurkan da Iran tun bayan da Donald Trump ya sanar da kammala ficewa daga yarjejeniyar nukiliyar da Tehran ta cimma da kasashen yammacin duniya inda a bangare guda ita kuma kasar ta fara karya ka’idojin da yarjejeniyar ta kunsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI