Amurka ke da damar kawo karshen tankiyarmu- Iran
Wallafawa ranar:
Shugaban Iran Hassan Rouhani ya shaidawa Amurka cewa ita ke da cikakkiyar damar kawo karshen takaddamar da ke tsakaninsu ta hanyar fara janye takunkuman da ta kakabawa Iran, matakin da ke zuwa lokaci kadan bayan Donald Trump na Amurka ya ce a shirye ya ke ya fara tattaunawa da Iran.
Cikin wasu kalaman kai tsaye da Rouhani ya gabatar da gidan talabijin din kasar, ya ce dole ne Amurka ta janye haramtattun takunkuman da ta kakabawa Iran wadanda shugaban ke cewa su ne mafarin tattaunawarsu da kuma warware rikicinsu.
A cewar Rouhani matukar Amurka ba ta dauki matakan warware rikicin ba, a shirye Iran take ta ci gaba da aikata abin da zai muzguna mata, musamman ta hanyar ci gaba da kokarin mallakar makamin nukiliya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu