Tsoffin 'yan tawayen Colombia sun sanar da sake daukan makamai
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Baraka ta kuno kai tsakanin tsofin 'yan tawayen FARC na kasar Colombia da gwamnatin kasar. A wani faye-faye bidiyo da aka yada a kafar Intanet ya nuna yadda jagoran kungiyar Ivan Marquez ke bayyana janyewa daga zaman sulhu da aka cimma da gwamnati a baya.
Jagoran kungiyar tawayen kasar Colombia FARC Ivan Marquez, ya sanar da yin fatali da yarjejeniyar sulhu da ta kai kungiyar ta ga rataba hannun ga batun sassantawa da zaman lafiya da hukumomin kasar .
Ivan Marquez a wani faye-faye bidiyo da ya aike ta shafin Youtube, ya na mai cewa suna sanar da Duniya cewa sun kaddamar da yaki mataki na biyu don nuna adawar su da rashin amincewa da mulkin danniya, hoton bidiyon ya kuma nuna wani jagoran 'yan tawayen na FARC Jesus Santrich dake kira ga yan kasar da su ba da hadin kai tareda daukar makamai.
Gwamnatin kasar ta Colombia yan lokuta da fitar da bidiyon, ta bayyana damuwa matuka ba, to sai dai tace bai bata mamaki.
Wani mai magana da yawun hukumomin kasar Ceballos ya bayyana karara cewa sanarwa daga magoya bayan wannan kungiya na tamkar tsokana da nuna rashin adalci ga kokarin hukumomin kasar da wasu amininta da ke kokarin samar da kwanciar hankali mai dorewa a kasar ta Colombia.
Iavan Marquez na wannan kira ne daga wani gundarin daji a yankin Kudu maso Gabashin kasar, ya na mai Allah wadai ga abin da ya kira rashin adalcin hukumomin kasar biyo bayan yarjejeniyar Havana ta shekarar 2017, da ta kawo karshen yakin fiye da shekaru 50 tsakanin 'yan tawayen da gwamnatin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu