Isa ga babban shafi
Jamus-Poland

Jamus ta nemi afuwar Poland kan ta'adin Yakin Duniya na 2

Wasu tankokin dakarun Adolf Hitler na Jamus, yayin kaddamar da farmaki kan kasar Poland, ranar 1 ga Satumba na shekarar 1939.
Wasu tankokin dakarun Adolf Hitler na Jamus, yayin kaddamar da farmaki kan kasar Poland, ranar 1 ga Satumba na shekarar 1939. AFP/File
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya nemi gafarar kasar Poland, bisa barnar da suka yi mata yayin yakin duniya na biyu shekaru 80 da suka gabata, lokacin da bama-baman ffarko da aka harba a yakin suka fada kan birnin Wielun dake kasar ta Poland.

Talla

A waccan lokacin dai Poland ce ta fi kowace kasa fuskantar tashin hankalin yakin duniyar na 2, la’akari da cewa ‘yan kasar kusan miliyan 6 ne suka halaka a yakin, wanda a jimilace yayi sanadin mutuwar mutane sama da miliyan 50.

Jimillar adadin kuwa sun hada da Yahudawa akalla miliyan 6, wadanda kusan rabinsu ‘yan kasar ta Poland ne.

A ranar 25 ga watan Agustan da ya gabata, Faransa tayi bikin cika shekaru 75 da kawo karshen mamayar da dakarun sojin Nazi, karkashin Adolf Hitler na Jamus, suka yiwa birnin Paris.

A rana mai kamar ta 25 ga watan Agustan 2019, cikin shekarar 1944, dakarun Faransa da hadin gwiwar ma’aikata, mata, har ma da limaman coci suka samu wannan nasara bayan shafe kwanaki 6 suna gwabza fada da dakarun na Nazi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.