Isa ga babban shafi
Hong Kong

Daliban Hong Kong sun kaurace wa makarantu

Wasu daga cikin daliban makarantun Hong Kong da suka shiga zanga-zangar adawa da gwamnatin yankin
Wasu daga cikin daliban makarantun Hong Kong da suka shiga zanga-zangar adawa da gwamnatin yankin REUTERS/Tyrone Siu
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 2

Dubban daliban makarantun sakandarer da na jami’o’i sun kaurace wa azuzuwa a ranar farko ta sbauwar shekarar komawa makaranta.

Talla

Wasu hotuna da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna daliban rike da hannayen juna a dogon layin da suka yi a harabar wasu makarantun sakandare da ke birnin na Honk Kong.

Wannan nna zuwa ne bayan jagororin masu zanga-zanga sun bukaci gudanar da yajin aikin gama-gari na tsawon kwanaki biyu tare da gudanar da gagrumnin gangami.

An yi arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an ‘yan sanda a karshen mako, yayinda masu boren suka cilla wa ‘yan sandan wutar aci-ba-bal, kana suka kai hari kan ginin majalisar dokoki.

Kodayake ‘yan sandan sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla da harsashen roba da ruwan zafi da zummar tarwatsa masu zanga-zangar.

Hong Kong na neman shiga mako na 14 a jere da fara gudanar da zanga-zangar da ta samo asali tun bayan da gwamnatin yakin ta sanar da aniyarta ta tasa keyar masu laifi zuwa China domin fuskantar hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.