Faransa

Faransa ta shiga tsakani kan rikicin Isra'ila da Hezbollah

An yi luguden wuta tsakanin mayakan Hezbollah na Lebanon da sojojin Isra'ila
An yi luguden wuta tsakanin mayakan Hezbollah na Lebanon da sojojin Isra'ila REUTERS/Stringer

Faransa ta gana da bangarori da dama da zummar magance tankiya tsakanin mayakan Hezbollah na Lebanon da sojojin Isra’ila kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar ta sanar.

Talla

Tun da fari Firaministan Lebanon, Saad Hariri ya bukaci Faransa da Amurka da su tsoma baki domin samar da kwanciyar hankali kan rikicin mayakan Hezbollah da Isra’ila, yana mai cewa, shugaba Emmanuel Macron ya gana da Benjamin Netanyahu da kuma shugaban Iran Hassan Rouhani a ‘yan kwanakin nan.

Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa ta fitar, ta ce, kasar ta gudanar da jerin ganawa da wasu bangarori a yankin tun bayan fara barkewar rikicin a ranar 25 ga watan Agusta da nufin dakile tsanantan tashin hankalin.

Sanarwar ta ce, Faransa na cikin ganawar din-din-din da masu ruwa da tsaki a Lebanon, sannan za ta kara kaimi a kokarin da ta ke yi na ganin kowanne bangare ya rungumi zaman lafiya.

A ranar Lahadin da ta gabata ne, Isra’ila da mayakan Hezbollah suka yi musayar wuta akan iyakar Lebanon bayan mako guda da tsanantar tankiyar, amma babu wanda ya samu rauni, yayinda Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a kai zuciya nesa.

Isra’ila ta ce, ta yi luguden wutar atilari har sau 100 bayan Hezbollah ta harba mata makamai masu linzami guda biyu zuwa uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.