Mata Falasdinawa sun gudanar da zanga - zangar neman yanci

Shugaban Yankin Falasdinu Mahmoud Abbas.
Shugaban Yankin Falasdinu Mahmoud Abbas. REUTERS/Mohamad Torokman

Dubban mata Falasdinawa ne suka gudanar da wata zanga-zangar neman ‘yanci a jiya Litinin, matakin da ke biyo bayan zargin dukan da ya hallaka wata matashiya a yankin wanda ake zargin iyayenta da aikatawa.

Talla

Dubun dubatar matan rike da kwalayen da ke dauke da rubutun neman ‘yanci tare da kawo karshen tsangwama ko kuma takura, sun rika sintiri a sassan yankin inda suke kalubalantar matakin yi musu iyaka a al’amuransu.

Zazzafar zanga-zangar irinta ta farko da yankin an Falasdinu ya taba fuskanta daga mata, ya biyo bayan zargin dukan Israa Grayeb da ake kan ahalinta bayan da suka zargeta da dora hoton da bai dace ba a shafukan sada zumunta, ko da dai tuni ahalin suka musanta.

Cikin bayanan da Ahalin Israa Ghrayeb suka bayar game da mutuwarta sun ce matashiyar mai shekaru 21 ta mutu ne sanadiyar shanyewar barin jikinta.

Sai dai wasu kafofin yada labaran yankin sun tabbatar da cewa Ghrayeb ta mutu ne sanadiyyar dukan da iyayenta da ‘yan uwanta suka lakada mata bayan dora wani hoto a shafinta na Instagram, hoton da aka goge shi daga shafin a jiya Litinin.

Rundunar ‘yansandan yankin dai ta bayyana cewa, kawo yanzu bata samu hujjar da ke nuna cewa Grayeb ta mutu ne sanadiyyar Duka ba, sai dai dubban masu zanga-zangar wadanda suka faro tun daga ranar Asabar din da ta gabata,na ci gaba da fafutukar ganin an kwatarwa matashiyar hakkinta, tare da bayar da cikakkiyar kariya ga sauran matan yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.