Duniya

Bincike ya gano masu hannu a yakin Yemen

Mutane da dama ne suka mutu a yakin Yemen
Mutane da dama ne suka mutu a yakin Yemen REUTERS/Mohamed al-Sayaghi TPX IMAGES OF THE DAY

Masu Binciken laifuffukan yaki na Majalisar dinkin Duniya sun bayyana takaicikan irin tashin hankalin da suka gani, wanda ya hada da kisa da azabtarwa da kuma fyade da akeyi ba tare da kaukautawa ba, a tashin hankalin dake gudana a Yemen.

Talla

Masu binciken da hukumar kare hakkin Bil Adama ta nada a shekarar 2017, sun bayyana gano wasu mutane da suka ce suna da hannu wajen aikata laifuffukan yakin kuma tuni suka gabatarwa Majalisar Dinkin Duniya da sunayen su.

Sanarwar masu binciken tace da zaran an tantance sunayen mutanen, ana iya gurfanar da su a kotun hukunta manyan laifuffuka domin fuskantar tuhuma.

Shugaban masu binciken, Kamel Jendoubi ya bukaci kasashen duniya da su daina kau da ido kan irin wannan cin zarafi da halin kuncin da mutanen Yemen ke ciki.

Tun bayan barkewar yakin a shekarar 2015, daruruwan mutane ne suka rasa rayukan su, yayin da al’ummar kasar suka fada cikin bala’in yunwa da tabarbarewar rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.