Isa ga babban shafi

Trump ya dakatar da tattaunawa da Taliban

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka Jabin Botsford/The Washington Post via Getty Images
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Shugaban Amaurka Donald Trump ya janye daga tattaunawar sirrin da ya shirya gudanarwa da wakilcin kungiyar Taliban bayan hare-haren kungiyar da ya hallaka sojoji ciki har da na kungiyar tsaro ta NATO.

Talla

Kafin harin dai a yau Lahadi ne Trump zai yi ganawar da wakilcin Taliban wadda aka tsara za ta gudana a Camp David fadar shugaban kasar da ke Maryland, a wani yunkuri na kawo karshen yakin Amurka a Afghanistan na kusan shekaru 20.

Cikin sakon Twitter da ya wallafa a yammacin jiya Asabar, Trump ya ce babu sauran batun ganawar sirrin.

Matakin janyewar na Amurka dai zai kawo karshen yunkurinta na shekara guda da ta shafe ta na mabanbantan tattaunawa da kungiyar ta Taliban bisa jagorancin jakadanta Zalmay Khalilzad wanda ke fatan kawo karshen yakinta a kasar tare da janye dakarunta.

Tuni dai shugaba Ashraf Ghani na Afghanistan ya yaba da kokarin Amurka tare da fatan ci gaba da aiki tare da samar da wanzajjen zaman lafiya a kasar mai fama da hare-hare ta'addanci baya ga kungiyoyi masu tsaurin addini.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.