Bakonmu a Yau

Dr Tukur Abdulkadir kan dakatar da tattaunawar Amurka da Taliban

Sauti 03:44
Tawagar wakilan Taliban.
Tawagar wakilan Taliban. KARIM JAAFAR / AFP

Shugaban Amurka Donald Trump ya jingine tattaunawar da kasar ke yi da Taliban ta Afghanistan bayan da ya zargi kungiyar da yiwa yarjejeniyarsu zagon kasa bayan kaddamar da sabbin hare-hare da ya kai ga kisan Sojin Amurka, tattaunawar da ke nufn kawo karshen yakin kasar na kusan shekaru 20. Ko meye makomar zaman lafiya kasar bayan wannan makay? tambaya kenan da Garba Aliyu ya yiwa Dr Tukur Abdulkadir masanin siyasar duniya na Jami'ar jihar Kaduna a Tarayyar Najeriya ga kuma amsar da ya bashi.