Amurka-Taliban

Kofa a bude take kan tattaunawarmu da Taliban- Pompeo

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo Eduardo Munoz Alvarez/Getty Images/AFP

Duk da matakin dakatar da tattaunawar sirri tsakanin Amurka da kungiyar Taliban wadda ta shafi hatta tattaunawar kawo karshen yakin Afghanistan da bangarorin biyu ke yi tsawon watanni, har yanzu kofa a bude take don ci gaba da tattaunawa daga bangarorin biyu.

Talla

Shugaba Donald Trump na Amurka bayan daukar matakin dakatar da ganawar a ranar Asabar, ya bayyana cewa ba shi da nufin kaddamar da yaki kan kungiyar don martani kan harin da ya hallaka sojin Kasar.

Yayin wata zantawar sakataren harkokin wajen Amurkan Mike Pompeo da manema labarai, ya ce kai tsaye a yanzu Amurka ba ta nemi ci gaba da tattaunawar amma a shirye ta ke ta amince matukar Taliban ta nuna a shriye ta ke a samu wanzuwar zaman lafiya a Afghanistan.

Donald Trump wanda ya zargi Taliban da yiwa tattaunawar ta su zagon kasa ya ce kungiyar a yanzu bata nuna cewa a shirye ta ke a kawo karshen yakin kasar ba.

Karkashin yarjejeniyar tattaunawar dai Amurka za ta janye dakarunta dubu 5 cikin dubu 15 da ke Afghanistan a badi, yayinda Taliban kuma za ta hada hannu wajen yakar sauran kungiyoyin ta’addanci da ke hargitsa tsaro dazaman lafiyar kasar.

A lahadin da ta gabata ne dai, Shugaba Donald Trump ya tsara wata ganawa da takwaransa na Afghanistan Ashraf Ghani da kuma kungiyar ta Taliban amma batun ya wargaje bayan harin kungiyar Taliban da ya hallaka mutane 16 ciki har da Sojin kasar ta Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.