Amurka

Majalisar Amurka na duba halascin shirin tsige Trump

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump © REUTERS/Joshua Roberts

‘Yan majalisar Amurka daga jam’iyyar Democrat, sun ce sun samu muhimmin ci gaba a yunkurinsu na tsige shugaba Donald Trump daga karagar mulki.

Talla

Duk da cewa wannan yunkuri na tsige Trump daga karagar mulki lamari ne da ya yi matukar raba kawunan ‘yan majalisar dokokin hatta a bangaren adawa, amma har yanzu akwai wadanda ke cewa ba gudu ba ja da baya a wannan yunkuri, daidai lokacin da ya rage shekara daya a gudanar da zaben shugaban kasa a Amurka.

Jerry Nadler shugaban Kwamitin kula da harkokin shari’a na majalisar wakilan wadda ‘yan Democrat ke da rinjaye, ya ce a ranar alhamis ta wannan mako za a fara bincike na shari’a dangne da halascin kaddamar da shirin tsige shugaba Trump.

An dai share tsawon watanni ‘yan majalisar na binciken Donald Trump bisa zargin cewa ya karya dokokin Amurka, laifin da matukar aka tabbatar da shi za a kaddamar da shirin tsige shi daga mukaminsa.

Wasu daga cikin zarge-zargen da ake yi wa Trump sun hada da yunkurin hana ruwa gudu lokacin da ake binciken Rasha da yin shisshigi a zaben da ya ba shi nasara shekara ta 2016, sai kuma zargin da ake yi wa shugaban na tsoma baki don ganin cewa wasu otel-otel mallakinsa sun rika samu kwangiloli bayan darewarsa karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.