Isa ga babban shafi
Amurka-Taliban

Amurka za ta ci gaba da farmakar Taliban a Afghanistan- Trump

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump © REUTERS/Joshua Roberts
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 min

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa dakarun kasar za su ci  gaba da kai munanan hare-hare kan maboyar mayakan Taliban da ke Afghanistan, kwanaki 5 bayan da shugaban ya soke tattaunawar da bangarorin biyu ke yi da juna.

Talla

Yayin da ya ke jawabi a wajen bikin cika shekaru 18 da harin ranar 11 ga watan Satumba da aka kai birnin New York, Donald Trump ya ce a cikin kwanaki 4 da suka gabata, dakarun Amurka sun kai munanan hare-haren da ba a taba gani ba kan mayakan na Taliban.

A cewar shugaban na Amurka, daga yanzu za su ci gaba da kaddamar da makamantan hare-haren a kowanne lokaci.

Trump ya ce an kaddamar da hare-haren ne bayan soke tattaunawar asiri da jami'ansa ke yi da Taliban a karshen mako, sakamakon harin da Taliban ta kai wanda ya kashe Sojin kasar guda daya.

Matakin soke tattaunawar dai na zuwa ne dai dai lokacin da ake gab da kulla yarjejeniyar kawo karshen yakin Afghanistan na kusan shekaru 20 wanda Amurkan ke yi a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.