Isa ga babban shafi
Amurka-China

Amurka zata sa ido kan muzgunawa yan kabilar Uighur daga China

Sansanin da ake tsare da yan kabilar Uighur a kasar China
Sansanin da ake tsare da yan kabilar Uighur a kasar China REUTERS/Thomas Peter/File Photo
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
1 min

Majalisar Dattawan Amurka ta amince da wani kudiri da zai yi matsin lamba ga gwamnatin China kan yadda take musgunawa yan kabilar Uighur, kudirin da zai baiwa gwamnatin Amurka damar sanya ido kan yadda ake tsare tarin yan kabilar da kuma azabtar da su.

Talla

Yan Majalisar sun amince da kudirin ba tare da hamayya ba, a karkashin dokar da suka yiwa suna ‘dokar kare yancin Yan Kabilar Uigur’ wanda ake fatar Majalisar wakilai ta amince da shi.

Kudirin zai baiwa ofishin leken asirin Amurka damar gabatar da rahoto a cikin watanni 6 kan yadda China ke tirsasawa Musulmi mazauna Xinjiang dake Yammacin kasar, inda akace China na tsare da akalla mutane miliyan guda daga cikin yan kabilun biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.