Iran ta musanta hannu a hari kan matatun man Saudiya

Shugaban Iran Hassan Rouhani
Shugaban Iran Hassan Rouhani 路透社。

Kasar Iran ta nesanta kanta da zargin Amurka na hannunta a harin jirage marasa matuka da ‘yan tawayen Houthi suka kaddamar kan matatun man Saudiya a jiya Asabar, inda Tehran ta yi zargin cewa Amurka na shirin kitsa manakisa ne kan batun.

Talla

Mai magana da yawun ma’aikatar wajen Iran Abbas Mousavi ya ce zargin na Amurka batu ne maras kan gado bayan rashin makama kan wanda za su tuhuma kan harin wanda ya kassara matatun man na Saudiya.

Sai dai sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce babu wata shaida da ke nuna hannun Houthi a harin duk kuwa da yadda suka dauki nauyinsa yana mai cewa Iran ce ta yi amfani da salon da ta saba wajen kaddamar da hari kan saudiya.

Yanzu haka dai harin ya kassara kashi 50 cikin dari na ayyukan hakar man saudiya matakin da ya rage adadin man da kasar ke fitarwa kasuwannin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.