Trump na duba yiwuwar ganawarsa da Iran bayan hari kan Saudiya

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Kevin Lamarque

Fadar shugaban kasar Amurka ta White House ta ce akwai yiwuwar Donald Trump ya gana da takwaransa na Iran Hassan Rouhani, duk da zargin da Amurka ke wa Iran na kitsa hari kan matatun man Saudiya ta hanyar amfani da ‘yan tawayen Houthi na Yemen.

Talla

Yayin zantawar ta da manema Labarai, Kellyanne Conway, mashawarciyar fadar shugaban kasar Amurkan ta White House, ba ta bayyana yiwuwar dakatar da ganawar tsakanin Donald Trump da Hassan Rouhani ba, dai dai lokacin da Saudiya ke kokarin farfado da matatar man na ta mafi girma a duniya bayan harin na Houthi.

A cewar Conmay wadda ke bayyana hakan ga sashen labarai na FOX a Amurka shugaban zai tsayar da matsaya game da tattaunawar yayin zaman majalisar Dinkin Duniya da zai gudana a birnin Newyork wanda a nan ne za a tabbatar da ganawar ko kuma kulla yarjejenniya don samar da maslaha ga bangarorin biyu da ke takun saka.

Amurkan dai na zargin hannun Iran a harin kan manyan matatun man Saudiya wanda ya kassara matatun baya ga rage yawan adadin man da kasar ke fitarwa kasuwanni duniya da akalla kashi 50 cikin dari, ko da dai tuni Iran ta musanta hannu a harin na ‘yan tawayen Houthi.

Sai dai sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce sun tabbatar da hannun Iran a harin wanda aka kai da jirage marasa matuka a safiyar asabar, duk kuwa da yadda ‘yan tawayen na Houthi masu samun goyon bayan Iran suka yi ikirarin kaddamar da farmakin.

Akwai dai hasashen iya samun jituwa tsakanin Amurkan da Iran musamman bayan ajje mukamin mashawarcin Trump kan harkokin tsaro John Bolton, sai dai ana ganin harin kan matatun man na Abqaiq mafi girma a duniya da kuma mai biye mata baya Khurais, ka iya haddasa tsaiko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.