Amurka-Saudi-Iran

Ba mu da nufin amfani da karfin Soji kan Iran-Trump

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka REUTERS/Kevin Lamarque

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana aniyar sa ta kaucewa yaki da kasar Iran, duk da barazanar daukar mataki kan kasar sakamakon harin da aka kaiwa cibiyar samar da man Saudi Arabia da Amurka ke zargin kasar.

Talla

Trump ya ce tabbas zai taimaki Saudi Arabia duk lokacin da aka kaiwa kasar hari, amma Amurka na jira a kammala bincike domin gano wanda ya aikata laifin, duk da ya ke alamu na nuna cewar Iran ce ke da alhakin kai shi.

Tuni kasashen duniya, irin su China da Rasha da kungiyar Tarayyar Turai suka bukaci taka tsan tsan wajen zargin Iran dangane da kai harin ba tare da kammala bincike ba.

Tun a ranar Asabar din da ta gabata, Donald Trump bayan tattaunawarsa da Yarima mai jiran gado na Saudiya Muhammad bin Salman shugaban ya ce a shirye kasarsa ta ke ta dauki fansar harin wanda 'yan tawayen Houth suka dauki alhakin kaiwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.