Muhalli-Tattalin Arziki

Kananan kasashe na bukatar magance gurbatar muhalli don yakar yunwa

Wasu mata yayin shuka irin noma a kauyen Mallamawa dake yankin Zinder.
Wasu mata yayin shuka irin noma a kauyen Mallamawa dake yankin Zinder. AFP

Wani Binciken masana ya bayyana cewar, kasashe matalauta na bukatar zuba jari wajen rage daina gurbata muhalli da kuma takaita amfani da ruwa domin samar da abinci mai gina jiki.

Talla

Masanan a Jami’ar Johns Hopkins dake Amurka sun samar da wata hanya kan yadda sauyin abincin da jama’a ke ci a kasashe 140 na duniya ke iya shafar yanayi da kuma tsaftacaccen ruwan sha ga daidaikun mutane da kuma kasa baki daya.

Rahotan da aka wallafa a mujallar muhalli ta duniya yace binciken yayi nazarin ne akan yanayin kowacce kasa da ruwan shan ta, da kuma abinda jama’a ke ci da suka hada da jan nama da ganyayyaki ba tare da janye kwai ba da madara da kuma makamantan su.

Keeve Nachman, babban jami’in da ya jagoranci binciken, yace akasarin tattaunawar da ake kan yadda za’a magance gurbacewar yanayi bai kula da cewar akasarin sassan duniya na fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI