Gutteress ya nemi daina ruwan bama-bamai a Syria da Libya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS/Brendan McDermid

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da shugaban kungiyar agajin Red Cross ta duniya Peter Maurer sun bukaci kawo karshen ruwan bama baman da ake samu a Syria da Libya wadanda ke matukar illa ga jama’a mazauna biranen Idlib da Tripoli.

Talla

Shugabannin biyu sun ce mazauna wadanann birane 2 na fuskantar matukar ukuba daga wadannan hare-hare, inda suka bukaci masu ruwa da tsaki cikin rikicin da su dakatar da kai hare haren.

Shugabannin sun ce dokokin duniya sun haramta kai hari kai tsaye kan fararen hula ko kuma matsugunan su da kuma garkuwa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.