Isa ga babban shafi
Duniya

Matasa na zanga-zanga a sassan duniya kan matsalar sauyin yanayi

Wasu daga cikin dubban matasan da suka shiga zanga-zangar neman tilastawa hukumomi daukar matakan magance matsalar dumamar yanayi.
Wasu daga cikin dubban matasan da suka shiga zanga-zangar neman tilastawa hukumomi daukar matakan magance matsalar dumamar yanayi. REUTERS/Jeenah Moon
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman | Abdoulaye Issa
Minti 2

Dubban matasa a sassan duniya sun kaddamar da zanga-zangar tilastawa hukumomi gaggauta daukar matakan magance matsalar sauyin yanayi.

Talla

Rahotanni sun ce zanga zangar da ta kunshi dalibai dasauran matasa da masu rajin kare muhalli, ta shafi akalla kasashe 150 na duniya.

Wasu daga cikin manyan biranen dake zama cibiyoyin zanga-zangar sun hada da Berlin, Canberra, Cape Town da kuma Kabul.

A Australia, zanga-zangar kan dumamar yanayi ta gudana a akalla birane da garuruwa 110, inda masu rajin kare muhallin suka bukaci gwamnatin kasar ta Australia ta rage yawan hayaki mai gubar da masana’antunta ke fitarwa, lakari da cewa kasar ke kan gaba a duniya, wajen fitar da makamashin Kwal da Iskar Gas.

Wadanda suka shirya zanga-zangar sun ce sama da mutane dubu 300, ne suka amsa kiransu a kasar ta Australia, tattaki mafi girma da aka gani a kasar, tun bayan makamancinsa da ya gudana ta adawa da Amurka kan afkawa Iraqi da yaki a 2003.

Ana saran Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya gudanar da wani taron gaggawa ranar litinin domin janyo hankalin shugabannin Duniya na ganin sun inganta alkawuran da suka dauka a yarjejeniyar Paris ta shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.