Isa ga babban shafi

Ukraine: An zargi fadar gwamnatin Amurka da rufa-rufa

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaran aikinsa na Ukraine Volodymyr Zelenskiy yayin wata ganawa a zauren taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 74.
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaran aikinsa na Ukraine Volodymyr Zelenskiy yayin wata ganawa a zauren taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 74. ©REUTERS/Jonathan Ernst
Zubin rubutu: Ahmed Abba
2 min

An zargi Fadar White House ta Amurka da kokarin boye nadaddiyar tatttaunawar wayar tarhon da shugaba Donald Trump ke matsin lamba ga Ukraine don ganin ta yi kasalandar a zaben shugabancin Amurka na shekara mai zuwa.

Talla

Kafofin yada labaran Amurka sun rawaito cewa, wani jami’in hukumar leken asirin kasar ta CIA ne ya fallasa batun tattaunawar wadda ta janyo yunkurin tsige shugaba Trump daga madafun iko .

Rahotanni sun ce, an ji Mr. Trump na matsin lamba ga takwaransa Volodymyr Zelensky don ganin ya gudanar da bincike kan Joe Biden da ke kan gaba wajen hamayya da Trump a Amurka.

Wannan na zuwa ne bayan da Majalisar wakilan Amurka ta bude sauraron basi da zummar tsige shugaba Trump daga karagar mulki, biyo bayan tattaunawa ta wayar tarho da shugaban na Amurka ya yi da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky, wadda aka ce ya saba wa rantsuwar da ya sha ta kama aiki.

A zaman da Majalisar Wakilan ta fara a jiya Alhamis, wani mai tonon silili ya ce fadar White House ta yi yunkurin boye rubutaccen bayanin tattaunawar tarhon na shugabannin biyu.

Mai tonon sililin ya ce tun da farko jami’ai a fadar White House sun nuna fargaba da irin tattaunawar da ta gudana tsakanin Trump da Zelensky.

Ya ci gaba da cewa kwanaki bayan tattaunawar shugabannin biyu ta tarho, labari ya ishe shi daga da dama cikin ma’aikatar White House cewa manyan jam’ien fadar shugaban kasar sun yi yunkurin shafe duk wani abu mai nasaba da tattaunawar.

Tuni shugaba Trump da fadar White House suka musanta aikata ba daidai ba, inda shugaba Trump da ya taho daga taron Majilsar Dinkin Duniya na 74 ya bayyana yunkurin tsige shi a matsayin wasan yara.

Kusa a jami’iyyar Democrats, kuma shugabar Majalisar Dokokin Amurka, Nancy Pelosi ta zargi fadar White House da yin rufa – rufa kan batun.

A jiya Alhamis jaridar New York Times ta Amurka ta wallafa labarin da ya nuna tana da masaniya kan mai tonon sililin, inda ta ce namiji ne, kuma ma’aikacin hukumar leken asirin Amurka da aka taba tura aiki a fadar shugaban Amurka

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.