Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon kamar yadda aka saba, yayi bitar manyan al'amuran da suka faru a sassan duniya cikin makon da ya gabata. Taron shugabanni da wakilan kasashe karo na 74 a zauren majalisar dinkin duniya, na daya daga cikin muhimman batutuwan da shirin na Mu Zagaya Duniya ya yi bita.