Amurka

Pompeo ya bijire wa umarnin majlisar dokokin Amurka

Sakataren wajen Amruka Mike Pompeo,
Sakataren wajen Amruka Mike Pompeo, REUTERS/Yuri Gripas/File Photo

Sakataren harakokin wajen Amruka, Mike Pompeo, ya ce a yinkurin tsige shugaban Amruka da ake yi, ma’aikatan ofishinsa da ya ce an tuntuba su bada bayanan karya kan shugaban Amruka Donald Trump, ba za su halarci gayyatar amsa tambayoyi da komin binciken badakalar na Majalasar dokokin ya yi masu ba a wannan mako.

Talla

Daukar wannan mataki ba ya na nufin bijirewa umarnin komitin bane gaba daya a’a, sai dai nuna turjiya ga yinkurin da majalisar ke yi na tsige shugaban kasar Donald Trump, wanda ya sa sakataren harakokin wajen yin watsi da lokacin da yan demokrat suka a shirya ganawar a karkashin yinkurin tsige shugaba Donald Trump daga kan karaga da aka kaddamar.

A cikin wata wasika da ya aikawa majalisar dokokin, sakataren harakokin wajen, Mike Pompeo ya ce gayyatar da aka yi wa jami’an diflomasiyar wata barazana ce, a da kuma kokarin wulakanta manyan jami’an diflomasiyar kasar masu daraja.

Pompeo ya ce, sakamakon damuwar da ake fuskanta kan bin tsari dokance, ba zai taba yiyiwa ba, jamian nasa su iya halartar majalisar dokokin domin bada bahasi a wannan mako.

Komitin da aka dorawa alhakin gudanar da binciken, ya aika da sammaci ga wasu jami’an diflomasiyar ofishin harakokin wajen Amruka domin su bada bahasi kan huldar aikin da ta shiga tsakanin shugaba Trump da kuma kasar Ukraine.

A yau laraba dai an shirya sauraren bahasi ne, kan tsohuwar jikadiyar Amruka Kiev. Shuwagaban komitcin uku a majalisar dokokin, nan da nan suka mayar wa da Mr Mike Pompeo amsar wasikarsa.

Inda suka bukaci Sakataren harakokin wajen da a cewa, a cikin gaggawa ya kawo karshen barazanar da yake yi wa shaidun, domin kare kansa da na shugaban kasar.

Domin a cewarsu sakataren harakokin wajen na Amrukar kai tsaye, ya na matsayin shaida ne, a binciken da ake yi.

Bugu da kari jami’an uku, sun danganta duk wani yinkuri na hana ma’aikatan harakokin wajen karba tamboyoyin majalisar, domin haifar da tarnaki ga yinkurin tsige shugaban kasar a matsayin taka doka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.