Mu Zagaya Duniya

Shirye-shiryen tsige shugaban Amurka ya soma kankama a majalisa

Sauti 20:01
Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. ©REUTERS/Kevin Lamarque

Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon kamar yadda aka saba, yayi bitar manyan al'amuran da suka faru a sassan duniya cikin makon da ya gabata, ciki har da halin da ake ciki kan binciken shugaban Amurka Donald Trump kan zarginsa da neman wata kasa ta yi katsalandan a zaben kasar na 2020. Sai kuma halin daake ciki kan sace dalibai 6damalamai 2 da 'yan bindiga suka yi daga wata makaranta a Kaduna.