Isa ga babban shafi
Amurka

An sake samun mai kwarmata bayanai kan Trump

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka ©REUTERS/Kevin Lamarque

Mutun na biyu daga cikin masu kwarmata bayanan sirrin da ka iya haddasa tsige shugaba Donald Trump daga karamar mulkin Amurtka, ya gabatar da kansa domin bayar da cikakken bayanin da ya tattara kai tsaye game da zantawar Trump da takwaransa na Ukraine.

Talla

Mutumin wanda ya gabatar da kansa a baya-bayan nan, jami’in leken asiri ne kuma tuni lauyoyin da ke kare shi suka gana da babban sufetan ‘yan sandan Amurka.

Sai dai ba a bayar da cikakkun bayanai kan mutumin ba.

Lauyoyinsa sun ce, mutumin na da bayanan da ya tattara kai tsaye kan zarge-zargen da ake yi wa Mr. Trump game da ganawar wayar tarho da shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky a ranar 25 ga watan Yuli, inda ya matsa masa da ya gudanar da bincike kan abokin hamayyarsa ta siyasa, Joe Biden, wato, tsohon mataimakain shugaban Amurka.

Yunkurin tsige shugaba Trump ya samo asali ne daga wannan tattaunawa da takwaransa na Ukraine bayan mutun na farko ya fara fallasa abin da shugabannin biyu suka tattaunawa akai.

Fadar White House, ba ta yi tsokaci kai tsaye ba, yayin da shugaba Trump ke ci gaba da musanta zargin da ake yi masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.