Amurka

Amurka ta kama bakin haure miliyan guda akan iyakarta

Wasu daga cikin bakin hauren da ke kokarin neman mafaka a Amurka
Wasu daga cikin bakin hauren da ke kokarin neman mafaka a Amurka Pedro PARDO / AFP

Amurka ta tsare bakin haure kusan miliyan guda akan iyakarta da kudancin Mexico a cikin watanni 12 da suka gabata. Wannan shi ne adadi mafi girma cikin sama da shekaru 10 da aka hana shiga kasar ta barauniyar hanya.

Talla

Amurka ta tsare ko kuma hana wadannan mutanen masu yawa ne a daidai lokacin da shugaba Donald Trump ya tsananta kaimi wajen dakile masu shiga cikin kasar ba bisa ka’ida ba.

Mukaddashin Darektan Hukumar Hana Fasa Kauri da Tsaren kan Iyaka, Mark Morgan ya ce, a cikin watan Satumba kadai, wanda shi ne watan da aka yi kamen karshe a bana, sun tsare bakin haure dubu 52, abin da ya bayyana da gagarumar nasara idan aka kwatanta da alkaluman da aka samu a shekarun baya.

Akasarin bakin dai sun fito ne daga kasashen yankin tsakiyar Amurka bayan sun guje wa talauci da tashe-tashen hankula, inda suke kokarin neman mafaka cikin dandazo a Amurka, yayin da suke ratsowa ta Mexico.

Gwamnatin shugaba Trump ta roki Mexico da ta agaza mata ta hanyar hana bakin kwararowa bayan sun baro kasashensu na asali da suka hada da Honduras da Guatemala da El Salvado.

Amurkar ta kuma bukaci bakin da su fara neman mafaka a hukumancce a kasar da suka fara kicibus da ita kafin ma su ce za su karaso cikin Amurkar.

Tuni dai fadar White House ta ci gaba da matsa kaimi wajen gina katuwar katanga akan iyakar kasar da Mexico mai tsawon mil dubu 2, inda ta karkata kudaden da aka ware wa Ma’aikatar Tsaron kasar domin gina wannan katanga wadda tun da farko majalisar dokoki ta yi watsi da batun samar da kudin gina ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI