NATO na fargabar yiwuwar Turkiya ta wuce makadi da rawa a Syria

Sojin Turkiya da ke ci gaba da kai farmaki don kakkabe mayakan Kurdawa.
Sojin Turkiya da ke ci gaba da kai farmaki don kakkabe mayakan Kurdawa. exodus. Nazeer Al-khatib/ AFP

Babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya bayyana damuwa a game da hare-haren da kasar Turkiya ke kai wa Syria, inda ya ce yana fatan Turkiya ba za ta wuce makadi da rawa ba a wannan farmaki.

Talla

Jens Stoltenberg, ya bayyana matukar damuwa a game da wadannan hare-hare da kasar ta Turkiyya ta kaddamar kan Kurdawa a cikin Syria, inda ya ce wannan farmaki ne da zai iya kawo cikas ga kokarin da kasashen duniya ke yi domin murkushe kungiyar IS.

Cikin jawabinsa Stontelberg ya ce akwai fatan Turkiyya ta sanya wa zuciya ruwa a wannan hari, bai kamata farmakin ya kawo cikas ga gagarumin aikin da muka yi a baya don yaki da IS ba.

Babban sakataren an NATO ya ce har yanzu IS na ci gaba da kasancewa barazana ga yankin Gabas ta Tsakiya, da arewacin Afirka da kuma sauran kasashen duniya.

A dai bangaren kuma sakataren tsaron kasar Amurka Mark Esper ya gargadi Turkiya da ta kawo karshin wannan kutse da ta kai a Arewa maso kudancin Syria, yana gargadin cewa wannan lamari zai iya haifar da mummunan sakamako ga kasar ta Turkiyya.

Mark esper ya yi wannan gargadi ne a zantawarsa ta wayar tarho da takransa na Turkiyya Hulusi Akar a wannan juma’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI