Syria-Turkiya

Kurdawan Syria sun nemi bai wa farar hula damar fita daga yankinsu

Tawagar motocin sojin Turkiya akan iyakar kasar da Syria
Tawagar motocin sojin Turkiya akan iyakar kasar da Syria REUTERS

Shugabancin mayakan Kurdawa a Syria ya bukaci kungiyoyin kare hakkin dan adam su sanya baki don bayar da damar fitar da tarin fararen hular da ke yankin da Sojin Turkiya suka yiwa kawanya akan iyakar kasashen biyu, bukatar da ke zuwa dai dai lokacin da IS ta sanar da sakin tarin matan da mayakan na Kurdawa suka kame.

Talla

A safiyar yau Alhamis ne, kungiyar IS ta sanar da sakin tarin matan da mayakan Kurdawan suka yi garkuwa da su, matakin da ke zuwa bayan fatattakar da Kurdawan ke fuskanta daga Sojin Turkiya.

Yayin da aka shiga kwana na 9 da kaddamar da farmakin na Turkiya wanda ya haddasa rarrabuwar kai tsakanin hatta manyan kasashen duniya da kungiyar tsaro ta NATO, IS a safiyar yau Alhamis ta bayyana cewa ta farmaki Shalkwatar Kurdawan da ke yankin Raqqa daren jiya Laraba tare da tseratar da tarin matan musulmi da mayakanta suka yiwa garkuwa da su.

IS wadda ba ta bayyana adadin matan ba, haka zalika ba ta fayyace ko matan mujahidai ne ko kuma mambobi ne na kungiyar ba, matakin na ta na zuwa dai dai lokacin da a bangare guda Mayakan na Kurdawa ke neman kungiyoyin jinkai sun sanya baki don baiwa fararen hula damar ficewa daga yankunansu, wanda a yanzu haka Sojin Turkiya suka yiwa kawanya don ci gaba da gwabza yaki.

Kiran na Kurdawa wanda ke zuwan bayan wani harin Sojin na Turkiya kan Asibiti da ya kai ga kisan jami’an lafiya da kuma majinyata, Tuni kungiyar kare hakkin dan adam ta Birtaniya da ke sanya idanu kan rikicin Syrian ta nemi sanya bakin manyan kasashe.

A bangare guda, Tuni Shugaba Bashar al Assad ya sake aikewa da tarin dakaru don tallafawa mayakan na Kurdawa a kokarin kasar na kubuta daga mamayar Turkiya.

Shima dai Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence yayin ganawarsada shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya nemi tsagaita wuta a farmakin Turkiyan wanda ya sake yamutsa kasar ta Syria a baya-bayan nan, sai dai kiran na sa na zuwa ne dai dai lokacin da Turkiya ta sake fadada farmakinta a yau Alhamis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI